Header Ads

Babban bankin Nijeriya ya amince a karbi tsofaffin takardun kudi

Gwamnan jihar Anambara, Farfesa Charles Soludo, ya tabbatar a ranar Litinin cewa babban bankin Nijeriya ya ba bankunan kasuwanci umarnin su karba kuma su bayar da tsofaffin takardun kudi.

Kamar yadda Daily Post ta ruwaito, Soludo, wanda tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya ne, ya bayyana hakan ne a shafin sa na sada zumunta.

Ya bayyana cewa gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele ne ya bayar da umarnin a yayin wata tattaunawa ta kwamitin masu bankuna a ranar Lahadi.

Ya kara da cewa Emefiele ya bayyana masa haka shi da kansa.

"An umarci bankunan kasuwanci da su bayar da tsofaffin kudi kuma su karba daga kwastomomi. Takardar saka kudi (Tellers) za su kasance da nambobin saka kudi, kuma ba ka'idar ko sau nawa mutum ko kamfani zai saka kudade.

" Gwamnan babban banki shi ya bayar da umarnin yayin tattaunawa da kwamitin masu bankuna a ranar Lahadi, 12 ga watan Macin 2023. Gwamnan, Dakta Godwin Emefiele, da kansa ya tabbatar da haka a gareni a yayin da na ke tattaunawa da shi ta wayar tarho a cikin daren Lahadi. Saboda haka mutanen da suke Anambara ina shawartarsu su karba tsofaffin kudi (N200, N500, N1000) hankalinsu kwance su yi kasuwanci da su tare kuma da sababbin kudaden." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

No comments

Powered by Blogger.