Header Ads

APC ta yi watsi da sakamakon zaben gwamna na jihar Bauchi

Dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar Bauchi, Air Marsha Abubakar Sadique da gwamnan jihar Bauchi, mai takara a jam'iyyar PDP, Bala Abdulkadir Mohammed

Jam'iyyar APC ta yi watsi da sakamakon zaben gwamna a jihar Bauchi da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana, inda jam'iyyar ta yi ikirarin akwai magudi a cikinsa.

Sakataren hulda da jama'a na kasa na jam'iyyar, Felix Morka, a cikin wani jawabi da ya yi, ya bukaci hukumar ta INEC ta yi bayani dangane da al'amurran dangwala kuri'u fiye da ka'ida, yin aiki da na'urar BVAS ba yadda ya kamata ba da fadace-fadace a wurare da dama a cikin jihar yayin gudanar da zaben na gwamna.

A jihar ta Bauchi dai, gwamnan Bala Muhammad na jam'iyyar PDP ne hukumar ta INEC ta bayyana ya yi nasara a zaben gwamna da aka yi a jihar da kuri'u 525,280 inda ya yi nasara a kan babban abokin takararsa, Air Marshal Abubakar Sadique Baba na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 432,272.

Sai dai jam'iyyar ta APC ta ce yadda abubuwan suka gudana akwai magudi.

"Ba za a iya musanta cewa an dangwala kuri'u fiye da ka'ida ba, cuwacuwa a yayin zabe a wurare da dama, ayyukan daba, barazana, tsoratarwa da fadace-fadace a wurare da dama a jihar Bauchi ba a yayin zaben gwamnan na jihar ta Bauchi.

" Jam'iyyar APC na kira ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta da ta yi bincike cikin rahoton da ke nuna cewa an yi amfani da na'urar BVAS ba yadda ya dace ba a rumfunan zabe sannan kuma ta soke sakamakon zaben da aka kara a rumfunan zaben da hakan ya faru da ke jihar.

"Musamman a kananan hukumomin Alkaleri, Kirfi, Toro, Warji, Ningi da Zaki da ke jihar inda aka samu fadace-fadace, dangwala kuri'u fiye da ka'ida da magudin zabe wadanda suka shafi dan takarar gwamna a jam'iyyar APC, Air Marshal Abubakar Sadique mai ritaya.

"Abin mamaki ne a ce an kirkiro alkaluman zabe masu yawan gaske a rumfunan zaben da ba a yi zabe ba kuma ba a kada kuri'u ba.

" An soke zaben rumfunan zabe masu yawa na yankin da jam'iyyar APC ke da karfi sosai ba tare da wani gamsasshen dalili ba, sai dai kawai domin a rage masa yawan kuri'u sannan a kara karfin dan takarar jam'iyyar PDP, gwamna mai ci, Bala Abdulkadir Mohammed." Kamar yadda jam'iyyar ta bayyana.

Jam'iyyar ta APC ta zargi jam'iyyar ta PDP da korar wakilanta a wasu rumfunan zaben, inda ta bayyana cewa musamman a Alkaleri, 'yan dabar jam'iyyar ta PDP sun kori wakilanta daga rumfunan zabe suka kasance su ke da iko a wuraren tare da dangwala kuri'u ba tare da tantancewar na'urar BVAS ba kuma an rubuta sakamakon zabe ba tare da an yi zaben ba kamar yadda doka ta tanada.

APC ta kara da cewa akwai wurin da wani kwamishina ma ya sayi kuri'u duk da cewa kowa na kallonsa kuma ga kyamarori na dauka.

"A wani al'amari mai ban mamaki da ya faru a wani wuri wanda wakilan jam'iyya suka dauka, an yi rahoton cewa akwai wani kwamishina mai ci a yanzu haka na PDP da aka dauka yana sayen kuri'u a fili a idanun kyamara, 'yan kasa sannan kuma da taimakon jami'an tsaro wadanda ke da nauyin kamawa su kuma tsare masu laifi domin gudanar da bincike da yanke hukunci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

"Jam'iyyar APC ta yi watsi da kirkirarrun alkaluman zaben da kuma bayyana gwamnan Bauchi mai ci da hukumar zabe ta yi, tana kuma kira ga hukumar da ta soke sakamakon wadannan wurare da aka bayyana inda aka samu dangwala kuri'u fiye da kima, lalata kayan zabe, barazana, tsoratarwa, fadace-fadace a wurare da dama da sauran abubuwan da suka shafi magudi kamar yadda ta ke da ikon duba yadda sakamakon zabe ya ke cikin kwanaki bakwai a karkashin shafi na 65 na dokar zabe." Kamar yadda APC din ta bayyana.

No comments

Powered by Blogger.