AN YI MUSABAKA A MAKARANTAR BAKIRUL ULUM POTISKUM
-Daga Yusuf Waliy
A yau Alhamis ne Makarantar Baqirul ulum Tahfizul Qur'an Potiskum suka gudanar da Musabakar karatun Alkur'ani mai girma.
An fara taron ne da misalin karfe 10 na safiya inda Malam Sani ya bude taron da addu'a. Sai aka ci gaba da gabatar da daliban wanda suka kai sama da mutum 60.
Malam Sadisu Yahuza, ya yi takaitaccen jawabi a wajen inda ya kawo cewar; "Alkur'ani shi ne Littafin da Allah bai aiko wani littafi da ya kai shi ba."
Ya kuma ja hankalin daliban da cewar "Ku godewa Allah da ya muku baiwar kasancewa masu karatun Alkur'ani." Malam Ali Dawasa ne ya rufe taron da addu'a.
Post a Comment