Header Ads

An yi asarar kwai sama da na naira biliyan 30 sakamakon shirin sauyin takardun kuɗi na CBN

Sama da kiret din kwai miliyan 15 wadanda kudinsu ya kai naira biliyan 30 aka yi asarar su sakamakon shirin babban bankin Nijeriya na sauya fasalin kudi a Nijeriya.

Kungiyar masu kiwon kaji a Nijeriya (PAN) ce ta bayyana haka a ranar Juma'a a Abuja a cikin wani jawabi da ta fitar ta hanyar shugaban ta na kasa, Sunday Onallo-Akpa.

Kamar yadda ya bayyana, kwayayen ba a sayar da su bane kuma sun lalace sakamakon masu saye basu da kudin da za su saya.

"Masu kiwon kaji a fadin kasa sun yi asarar kiret din kwai sama da miliyan 15, ba a sayar da kwayayen ba kuma sun lalace, masana'antar kiwon kaji a yanzu haka a lokacin fitar da wannan jawabi ta yi asarar kudi sama da naira biliyan 30." Kamar yadda ya bayyana, inda ya kara da bayyana cewa masana'antar tana gaf da rushewa sakamakon shirin na sauya fasalin kudi.

Shugaban kungiyar, wanda ya bayyana yadda masana'antar ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzuki, ya bayyana cewa masana'antar hanya ce ta samar da ayyukan yi da karfafawa ga iyalai, musamman mata da matasa.

Shugaban sai ya yi roko ga sashen zartarwa na shugaban kasa da ya bayar da umarni ga hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA), Hukumar wanzar da zaman lafiya a Nijeriya ta sojoji da kuma shirin saka jari na Ma'aikatar Ayyukan Jin Kai da Agajin Gaggawa da su yi aiki da kungiyar a kan yadda za a samar da tallafi ga masu kiwon kajin da ke fadin kasa baki daya domin hana masana'antar rushewa. 

Sai ya kara da rokon gwamnati da ta samar da tallafi kai tsaye da kuma na kudade ga masana'antar ta hanyar kungiyar ta hanyar tsara wani shiri wanda kungiyar da gwamnati za su tsara a tare.

No comments

Powered by Blogger.