Header Ads

An kame daruruwa a yayin da mutane sama da miliyan daya ke zanga-zanga a birane 300 na Faransa

Wasu masu zanga-zanga a kasar Faransa

An kama daruruwan masu zanga-zanga a yayin da daruruwan jami'an tsaro suka jikkata yayin da mutane sama da miliyan daya ke gudanar da zanga-zangar kin amincewa da tsarin fansho na shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron.

Kamar yadda ministan harkokin cikin gida na Faransa, Gerald Darmanin, ya bayyana, an kama mutane 457 inda kuma jami'an tsaro 441 suka jikkata, kuma an kunna wuta har sau 903 a kan titunan Paris a cikin wata rana wadda ta fi kowacce yamutsi tun bayan watan Janairu. 

Dakin taro na The porch of the Bordeaux, wanda a nan ne aka shirya karbar sarkin kasar Ingila, King Charles III, a cikin sati mai zuwa shima an sa masa wuta da yammacin ranar Alhamis.

Zanga-zangar, wadda a yanzu ta shiga cikin kwana na tara kuma wadda mafiyawanci ta zaman lafiya ce, ta haifar da cikas ga tafiye-tafiyen jiragen kasa da na sama.

Ministan harkokin cikin gidan na Faransa ya bayyana cewa kimanin mutane 119,000 suka yi zanga-zanga a Paris, wannan kuwa shine yawan mutane da ya fi yawa a birnin kasar tun bayan fara zanga-zanga a kan fansho a kasar.

An dai yi imanin cewa tsakanin mutane miliyan 1 zuwa miliyan 3.5 suka gudanar da zanga-zanga a birane 300 da ke fadin kasar a ranar Alhamis.

'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa tare da kai farmaki ga masu zanga-zangar wadanda suka fusata sakamakon shirin Macron na kara shekarun ritaya daga 62 zuwa 64.

Malaman makarantu suna daya daga cikin ma'aikata kwararru da suka bar ayyukansu.

Kididdigar ta nuna cewa kusan kashi 70 cikin 100 na 'yan kasar Faransa sun yi watsi da shirin fansho din na Macron, to amma shi ya kafe cewa shirin ya zama dole domin mayar da tsarin mai tattali. 

Kungiyoyin ma'aikata sun kara yin kira da a gudanar da wata zanga-zangar a ranar Talata, kuma ranar ta zo daidai da ranar da sarkin Ingila, King Charles III, zai kawo ziyara kasar.

Kamar yadda masu sa ido kan yadda al'amurra ke gudana suka bayyana, wannan yamutsin shi ne yamutsi mafi girma wanda ke yin barazana ga mulkin Macron tun bayan zanga-zangar Yellow Vests a cikin watan Disambar shekarar 2018.

No comments

Powered by Blogger.