Header Ads

An bayyana wani mutum ba ya da laifi bayan ya kwashe shekaru kusan 35 a kurkuku a Amurka

Sidney Holmes

An gano cewa wani bakar fata dan kasar Amurka ba ya da laifin da zai sa ya kasance cikin kurkuku bayan ya kwashe shekaru kusan 35 a kurkuku.

Mutumin mai suna Sidney Holmes, wanda a yanzu shekarunsa 57, ana zarginsa ne da aikata fashi, inda a yanzu aka bayyana an wanke shi daga wannan zargi.

An dai kama shi ne a shekarar 1988, inda kuma a cikin shekarar 1989 kotu ta zarge shi da kasancewa direba ga wasu mutane biyu wadanda suka yi fashi ga wani mutum da kuma wata mata ta hanyar nuna masu bindiga.

Holmes, wanda ya yi kusan shekaru 35 a kurkuku cikin shekaru 400 da aka yanke masa, ya samu kubuta ne bayan jihar Florida da ke kasar ta Amurka ta yanke shawarar gudanar da bincike cikin zargin aikata fashi da ake yi masa inda ake ikirarin shine direban da ya gudu da wasu 'yan fashi a mota.

Harold Pryor, wanda shine Antoni na yankin Broward, ya bayyana cewa Holmes ya dage cewa shi bai aikata laifin da ake zargin ya aikata ba, shine sai ya Proyer din ya tuntubi sashen yin duba cikin zarge-zarge na jihar a cikin watan Nuwambar shekarar 2020, kuma suka amince tare da fara yin bincike cikin shari'ar.

"Alkalai da ke sashen da ke yin duba cikin zarge-zarge (CRU) sun ga alamun Holmes na iya kasancewa mara laifi sakamakon shaidar da ta sa ake zarginsa din ba ta karfi, kuma shaidar ce babbar madogara a cikin shari'ar da ake yi masa." Kamar yadda Pryor ya bayyana.

Sai kuma sashen yin bincike cikin zarge-zargen ya gano cewa mutanen da suka kasance shaidu kan al'amarin "ba su yi bayani da kyau" dangane da Holmes din ba, kuma matakan da jami'an tsaro suka bi wurin yin bayanin Holmes din "ba za a iya dogara da su a kimiyyance ba."

Jami'an tsaro a Florida, wadanda sune suka gudanar da binciken na asali, sun nuna "razanarsu" ganin cewa an saka Holmes a kurkuku sakamakon laifi wanda ba ya da alhakin aikatawa.

No comments

Powered by Blogger.