Header Ads

Amurka ta kakaba sabbin takunkumi kan Iran, wannan karon a kan wasu kamfanoni da wasu mutane

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden da shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ebrahim Raisi

Kasar Amurka ta kakaba takunkumi a kan wasu kamfanoni hudu da wasu mutane uku saboda ikirarin ta na hannun da suke da shi wajen kawo kayayyaki domin taimakon aikin jiragen yaki marasa matuka da Iran ke yi.

Kamar yadda rahoton ya nuna, wadanda wannan takunkumi ya shafa a kasar Iran da Turkiyya suke, kuma suna cikin aikin "kawo kayayyaki, wadanda suka hada da injina na asali daga kasashen turai na jiragen yaki marasa matuki domin taimakon aikin Iran na kera jiragen yaki marasa matuka da kuma shirin ta na makamai." 

Takunkumin ya dakatar da duk wata dukiyar Amurka ta wadanda abin ya shafa kuma ya haramtawa 'yan kasar ta Amurka yin hulda da su.

Dama a farkon wannan watan, Amurka ta sa takunkumi a kan wani "network" na kasar Sin wanda ta yi ikirarin na taimakawa shirin kasar Iran na kera jiragen yaki marasa matuka.

Wannan takukumi dai na zuwa ne a yayin da Amurka ke cikin zargin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da samar da jiragen yaki marasa matuka ga kasar Rasha domin ta yi amfani da su kan kasar Ukraine.

Ministan harkokin kasashen waje na Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya bayyana cewa Iran ta samar da jiragen yaki marasa matuka 'yan kadan ga Rasha, to amma samar da su din an yi shi ne watanni kafin a fara yakin na Ukraine.

No comments

Powered by Blogger.