Header Ads

Amurka da Isra'ila na son bakanta Musulunci a idon duniya - shugaban Ansarullah

Shugaban kungiyar Ansarullah, Al-Maliki al-Houthi

Shugaban sananniyar kungiyar nan da ke Yemen mai suna Ansarullah, Abdul-Maliki al-Houthi, ya yi Allah wadai da kokarin da Amurka da Isra'ila ke yi domin bakanta musulunci a idanun duniya tare da kokarin yin hari ga duniyar musulmai ta cikin gida. 

Abdul-Malik al-Houthi ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da ya ke gabatar da jawabi ga wasu malaman addini a babban birnin kasar wato Sana'a.

Ya yi kira ga malaman addinin da sauran masana da su kasance cikin kula domin tunkarar makirce-makircen da makiyan musulunci suka shirya, inda ya bayyana cewa a yanzu haka suna cikin bangarorin "sojoji, siyasa, tsaro, tattalin arzuki da bangaren al'adu" kuma suna yin amfani da duk damar da suka samu domin cimma manufofinsu.

"Akwai makircin hari ga duniyar musulunci ta cikin gida, kuma akwai malamai da dama da suke a kasashen musulmai da suke tare da Amurka da kuma Isra'ila wadanda ke so su bakanta musulunci." Kamar yadda Houthi ya bayyana. 

Shugaban Ansarullah din ya bayyana cewa makiya musulunci na son cutar da kasashen musulmai su kuma karkatar da su domin su haifar da rashin amincewa da kuma karkatar da addini.

Shugaban ya ma yi kira ga malaman addini na kasar Yemen din da su "farfado da al'adar yin taimako a cikin al'umma da kuma karfafawa mutane su taimaki masu neman taimako."

Tun da fari, Abdul-Malik al-Houthi ya kira Amurka da Isra'ila da "makiya namba ta daya" ga musulmai da ke fadin duniya.

"Amurka da Isra'ila na so su yi amfani da matsalolin da ke cikin Kasashen musulmai domin cimma makirce-makircensu." Kamar yadda ya bayyana a cikin watan Fabrairu yayin da ya karbi tawagar wakilan yarurruka daga bangarorin kasar da yaki ya yiwa illoli.

"Isra'ila da magoya bayan ta suna kallon Yemen a matsayin makiyyiyar su baki daya." Ya kara da cewa.

Shugaban na nufin kasashen larabawa wadanda suka hadu domin daidaita alaka da Isra'ila karkashin goyon bayan Amurka, tun lokacin kuma suke kokakin hada manufofinsu da na ta.

"Matsayar da masarautar Hadaddiyar Daular Larabawa, Isra'ila da kuma Saudiyya suka dauka a yayin tattaunawarsu a fili ta ke." Kamar yadda shugaban na Ansarullah ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.