Header Ads

A Sakkwato an yi gangamin Allah Wadai da ta'addancin El-Rufai

A safiyar yau Juma'a 17/3/2023 'yan uwa Musulmi a garin Sokoto suka fito gangamin Allah wadai da ta'addancin Gwamnan Kaduna, Nasiru Rufa'i, wanda a jiya Alhamis ya ba jami'an tsaronsa umurnin buÉ—e wa 'yanuwa musulmi wuta a Kaduna, suka kashe mutane kimanin takwas, shida almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky, da biyu cikin mutanen gari da ba su ji ba, ba su gani ba.
Elrufai ya shahara wajen ayyukan ta'addanci da take hakkin yan kasa, a yayin da ya tsanantawa al'ummar jihar Kaduna da raba da damansu da ayyukansu na gwamnati a bangarorin daban daban, da kuma tsauwalawa dalibai kudin makaranta, da rusa muhallai da kuma kashe raunanan al'ummar da ke neman hakkinsu da aka take musu.
Irin wannan gangamin na Allah wadai ya gudana a wasu garuruwa baya ga Sakkwato, daga ciki har da jihar Bauchi, wanda a safiyar yau suma suka fito Muzaharar, tare da kira ga gwamnatin Buhari da ta baiwa Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Passport dinsu don su samu damar fita wajen don neman lafiya, tunda ba wata doka da ta kange su daga hakan in banda kama-karya.

No comments

Powered by Blogger.