Header Ads

Zartar da Hukuncin kisa ya nunku a mulkin Salman da dan sa a Saudiyya Cewar Sabon rahoto


Sarkin Saudiyya da dansa Yarima mai jiran gado MBS

Yawan hukuncin kisa da ake yankewa mutane a masarautar Saudiyya na kusa lunkuwa a duk shekara tun bayan da sarki Salman da dan sa Yarima Mohammed bin Salman suka hau karagar mulkin masarautar a shekarar 2015, wanda hakan ke yin nuni da irin take hakkokin dan Adam da ake yi a masarautar.

Kamar yadda wani sabon rahoto daga Reprieve da kuma European Saudi Organisation for Human Rights (ESOHR) suka fitar ranar Talata ya nuna, akalla mutane 1,243 aka zartar da hukuncin kisa a kansu a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2021 a yayin da a shekarar da ta gabata kawai yawan mutanen ya kai 147.

Rahoton ya bayyana cewa shekaru guda shida da aka fi shekar da jini a Saudi Arabiya na 2015, 2016, 2017, 2018, 2019 da 2022 duka a karkashin mulkin Yarima Mohammed bin Salman ne a matsayinsa na Yarima mai jiran gado.

Rahoton ya nuna cewa akwai akalla hukuncin kisa 129.5 a kowacce shekara a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2022, wanda hakan na nuni da karin kashi 85 cikin 100.

Rahoton Reprive na shekarar 2023 mai taken "Shekar da jini da karairayi: Masarautar Mohammed bin Salman ta yanke hukunce-hukuncen kisa" ya nuna cewa daga shekarar 2010 zuwa 2021 wadanda aka samu da laifin kisan kai, safarar miyagun kwayoyi, laifukan da suka shafi badala, kirkirowa ko shiga kungiyoyin aikata laifuka, sacewa ko kullewa a kurkukun karya tare da azabtarwa, kwashe kayayyakin wani wuri ko yin fashi, yin maganganun da za su harzuka mutane, cin amanar kasa da sauran laifuffuka a kasar da maita da yin tsafe-tsafe dukkaninsu an yanke masu hukuncin kisa.

Rahoton ya kara da cewa shekarar 2021 itace shekarar da aka fi shekar da jini a cikin ta a cikin tarihin Saudi Arabiya na baya-bayan nan inda a rana daya aka yankewa mutane 81 hukuncin kisa, wato ranar 12 ga watan Maci na shekarar.

Kungiyoyin kare hakkin na 'yan Adam sun bayyana cewa ba za a iya sanin hakikanin yawan mutanen da ake yankewa hukuncin kisan ba domin hukumomin Saudiyyar ba su bayar da bayanai dangane da yanke manyan hukunce-hukunce saboda a asirce suke barinsu.

Binciken da Reprive ta gabatar ya nuna cewa hukunce-hukunce musamman wadanda suka shafi kisa a boye ake yinsu, ba a yarda a wallafa takardun kotu, ana canza caje-caje da ake yiwa mutum kuma ana dage sauraron shari'a ba tare da kayyadajjen lokaci ba.

Rahoton ya kara nuna cewa a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2021, Saudi Arabiya ta yankewa 'yan kasar waje 490 hukuncin kisa, kashi 39 kenan cikin dari na kisan da ta yi a tsakanin wadannan shekarun, hakazalika mata 31 ta yankewa hukuncin kisa a cikin shekarunnan kuma kashi uku cikin hudu duk 'yan kasar waje ne, kashi 56 masu aikin cikin gida ne.

Kungiyoyin sun bayyana cewa Mohammed bin Salman da majalisarsa suna so su kawar da hankulan mutane daga take hokkokin da suke yi ta hanyar wasannin, misali sayen kungiyoyi irinsu Newscastle United da shirya da gasa irinsu LIV Golf Tour a yayin da a bangare guda suna aikata wasu daga cikin munanan take hakkokin 'yan Adam a duniya ta hanyar yanke hukunce-hukuncen kisa ga mutane masu yawa.

No comments

Powered by Blogger.