Header Ads

Zaɓen 2023: An kirkiro shafin INEC na bogi a intanet


Magoya bayan ƴan hammaya a zaɓen Najeriya a shafukan sada zumunta da muhawara suna zargin cewa mutane sun yi kutse a shafin hukumar zaɓen ƙasar inda suke sanya sakamakon zaɓe na ƙarya.

Sai dai shafin da ake zargin cewa an yi kutsen ana sanya sakamako na ƙarya, ba ainahin shafin INEC ba ne, shafi ne shi kansa na bogi wanda aka ƙirƙira aka kuma tsara, ta yadda ya yi kama da na hukumar, kuma ake ta yaɗa shi.

Nazarin da sashen binciken ƙwaƙwaf da tantance labaran gaskiya daga na bogi na BBC, wanda ya gano hakan, ya yi, ya kuma gano cewa shi kansa adireshin shafin na bogi ba ɗaya yake da na hukumar zaɓen ba, sannan yana tattare da kura-kurai kamar yadda aka saba gani a yawancin shafuka na bogi.

A dangane da haka za a iya cewa ba wata shakka ko alama a yanzu ba wani kutse da aka yi wa shafin hukumar zaɓen Najeriyar, kamar yadda da dama wasu suke yarda.

Bayan wannan ma akwai kuma wasu rahotannin da ake ta yaɗawa cewa, INEC ta yi amfani da na'urarta ta tantance masu zaɓe wajen yin maguɗi, inda ake ta yada waɗannan labarai a shafukn sada zumunta na muhawara.

Wannan ne ma har ya sa wasu magoya bayan 'yan hamayya ke barazanar tayar da tarzoma idan dan takararsu bai ci zaɓe ba.

To amma gaskiya ne cewa na'urar ta kasa aiki a wasu wuraren zaɓen a ƙasar saboda wasu matsaloli nata ko kuma rashin intanet.

Wasu fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta na yaɗa cewa hukumar zaɓen ƙasar da kuma jam'iyya mai mulki APC za su yi maguɗi a zaɓen na 2023, wanda hakan ke sanya shakku a kan 'yancin-kai da kuma gaskiyar hukumar.

No comments

Powered by Blogger.