Header Ads

Zaben 2023: Tinubu ya yi nasara a jihar Kwara, Atiku a jihar Gombe


Tinubu da Atiku

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, shi ne ya yi nasara a jihar Kwara, kamar yadda BBC ta ruwaito jami'in tattara sakamakon zabe a jihar ya sanar a Ilorin. 

Kamar yadda ya sanar, kuri'un da manyan jam'iyyu suka samu sune jam'iyyar APC ta samu kuri'u 263,572, jam'iyyar PDP 136,909, jam'iyyar LP 31,166 sai kuma jam'iyyar NNPP mai kuri'u 3,141.

A jihar Gombe kuwa, hukumar ta INEC ta bakin jami'a mai tattara sakamakon zabe a jihar, Farfesa Maimuna Waziri, ta bayyana cewa Alhaji Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ne ya samu nasara a jihar.

Kamar yadda ta bayyana, sakamakon shine jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 319,123, APC 146,977, NNPP 10,520, jam'iyyar LP 26,160.

Sauran jam'iyyu a jihar ta Gombe su kuma sun samu 7,263.

Farfesar ta bayyana cewa yawan masu zabe da aka yiwa rijista a jihar sune 1,549,243, wadanda aka tantance 542,997, kuri'un da aka kada da kyau sune 510,043, wadanda suka lalace 23,735. 

A jihar ta Gombe dai bakidaya, yawan wadanda suka kada kuri'a shine mutane 533,778.

No comments

Powered by Blogger.