Header Ads

Zaben 2023: Mutane nawa suka mutu bayan kai hari a wani ofishin jam'iyyar NNPP da ke jihar Kano?


Gwamna Ganduje na jihar Kano

Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da aka kai a ofishin wani dan takarar majalisar wakilai ta kasa na jam'iyyar NNPP a jihar Kano.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda, SP Abdullahi Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, ya ce wani gungun mutanen da ake zargi batagari ne suka sawa ofishin wuta a cikinsa kuma akwai wata mota mai dauke da mutane biyu wadanda ba a iya fayyace ko su waye ba, mutanen kuwa sun kone kurmus.

Hukumar 'yan sandan jihar ta Kano ta bayyana cewa ta samu labarin afkuwar al'amarin ne da misalin karfe 4 na yamma a yayin da ake karbar sakamakon zabe a ofishin hukumar zabe ta karamar hukumar Tudun Wada.

"Ba bata lokaci muka tura jami'an tsaro zuwa wurin." Jami'in ya bayyana, inda ya kara da cewa ana cigaba da bincike kuma hudu daga cikin wadanda suka kawo harin an kama su, daya kuma cikin wadanda suka kawo harin ya yi mummunan rauni inda ya rasu a asibiti yayin da ya ke samun kulawa.

A wani al'amarin mai kama da wannan, 'yan sandan sun yi kokarin dakile wani yunkuri na kona ofishin zaben karamar hukumar Takai a yayin da ake tattara sakamakon zabe.

Wannan al'amarin kuwa ya faru ne da misalin karfe 2:30 na rana.

Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa ba bata lokaci suka dakile harin tare da kama wadanda ake zargin batagari ne mutum hudu. 

"An dai gama tattara sakamakon zaben lafiya kuma ana cigaba da bincike." Kamar yadda ya bayyana a cikin jawabin.

No comments

Powered by Blogger.