Header Ads

Zaben 2023: Jam'iyyun LP, PDP da ADC sun bukaci a sake sabon zabe kuma shugaban hukumar INEC ya sauka daga mukaminsa


Wakilan Jam'iyyun adawa

Jam'iyyun PDP, LP da ADC a yayin wani taron hadin gwiwa da suka gudanar a ranar Talata a Abuja, sun bukaci a sake gudanar da sabon zabe kuma shugaban hukumar INEC ya sauka daga kan mukaminsa, inda suka bayyana cewa zaben na shugaban kasa da 'yan majalisu da aka gudanar ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, na cike da kura-kurai, yin barazana da rikice-rikice. 


Jam'iyyun wadanda suka bayyana cewa hukumar INEC ta karya ka'idojin zaben wadanda za su tabbatar da sahihancinsa tun ma kafin a fara tattara sakamako, sun bayyana cewa, "Sashi na 60 karamin sashi na 5 na dokar zabe ta tanadar cewa jami'in da ke kula da zabe ya tura sakamakon zabe, hade da yawan mutanen da aka tantance da sakamakon takardun kuri'u kamar yadda hukumar ta tsara.

"Rashin bin wannan ka'ida ta dokar zabe da tsare-tsare za ta sa kenan dole duka wani sakamakon da aka sa a shafin IReV a maida sa cikakke a yadda ya ke kafin a fade shi.

"INEC ta kasa cika wannan alkawarin... Wannan zaben ba ingantacce ba ne kuma ba a yiwa kowa adalci ba.

"Ba za mu cigaba da kasancewa a matattarar zabe ta kasa ba kuma muna neman a soke wannan zaben.

"Muna kuma kira da a sake sabon zabe a bi dokoki kamar yadda hukumar zaben ta tsara.

"Saboda haka muna kira ga Yakubu da ya sauka daga mukaminsa." Shugaban jam'iyyar LP na kasa, Julius Abure, ya bayyana.

Jam'iyyun dai sun bukaci Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga mukaminsa kuma wani "amintacce" ya hau wanda ba cikin hukumar ya ke ba wanda zai dawo da fatar kowa da kowa, kasashen waje da kuma duka damakaradiyya.

Jam'iyyun, wadanda suka bayyana cewa miliyoyin 'yan Nijeriya sun sa fatar su a kan su da kuma 'yan takarar shugaban kasarsu domin hana wadanda ke neman haifar da wargajewa cimma nasara, sun bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya nuna karfin ofishinsa ya kuma tabbatar da kalamansa na samar da ingantaccen zabe, inda suka nemi hadin kan 'yan Nijeriya domin tseratar da damakaradiyyar Nijeriya.

A wurin taron, bayan shugaban jam'iyyar LP na kasa, Julius Abure, wadanda suka halarta sun hada da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu da kuma shugaban jam'iyyar ADC na kasa, Ralp Nwosu.

No comments

Powered by Blogger.