Header Ads

Zaben 2023: Atiku ya yi nasara a kan Tinubu a jihar shugaban kasa ta Katsina


Atiku da Tinubu

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi nasara a kan abokin takarar sa na jam'iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, a jihar shugaban kasa ta Katsina.

Muazu Abubakar, wanda shine jami'in da ke da alhakin bayyana sakamakon zabe a jihar, ya bayyana cewa Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri'u 489,045 inda shi kuma dan takarar shugabancin kasar a jam'iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, ya samu kuri'u 482,283 fadin jihar, banbancin da ke tsakaninsu kuwa shine 6,762.

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, kuri'u 69,386 ya samu a jihar.

 A jihar ta Katsina, duk da cewa dan takarar ta APC ya yi nasara ne a kananan hukumomi 21, shi kuma na jam'iyyar PDP a kananan hukumomi 13, to amma kuri'un dan takarar na PDP ne suka yi rinjaye. 

A cikin birnin Katsina, inda nan ne mahaifar tsohon shugaban kasa, marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua, dan takarar jam'iyyar ta PDP ya samu kuri'u 45,390 ne shi kuma na APC, Ahmed Bola Tinubu, ya samu 15,953.

Atiku Abubakar ya yi nasara a jihar Katsina duk da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da minstan jiragen sama, Hadi Sirika, duk daga jihar suke kuma gwamnan jihar, Aminu Bello Masari dan jam'iyyar APC ne.

No comments

Powered by Blogger.