Header Ads

Yara sama da 3,000 masu kansa sakamakon yakin Saudiyya a Yemen na cikin hatsarin rasa rayukansu - Kungiyar kare hakkin dan Adam

Wata 'yar Yemen mai fama da cutar kansa

Wata kungiyar kare hakkokin dan Adam da ke kasar Yemen ta yi gargadin cewa yakin da Saudi Arabiya ke yi a kasar da kuma kulle iyakokin kasar wadda ke cikin tsanani na iya haifar da mutuwar dubunnan yara masu fama da cutar kansa.

Kungiyar mai suna Entisaf Organization for Women's and Children Rights, ta bayyana haka ne a cikin wani jawabi a ranar kansa ta duniya, wato World Cancer Day, inda ta ce sama da yara 3,000 'yan kasar Yemen wadanda suka kamu da cutar kansa sakamakon yakin Saudi Arabiya a kan kasar da kuma kulle iyakokin teku, kasa da sama, a yanzu haka na cikin hatsarin rasa rayukansu. 

Kungiyar kare hakkin ta nuna rashin jin dadinta da yadda manyan kungiyoyin duniya suka ki nuna kulawarsu ga masu fama da cutar kansa da ke Yemen.

Kungiyar ta kara da cewa yawan masu samun cutar kansar cikin jini (Leukemia) na kara hauhawa a tsakanin yara a kasar Yemen, inda ta bayyana cewa yanzu yawan yara masu cutar ya haura daga 300 zuwa 700 a birnin Sana'a saboda yin amfani da makaman da gabakidaya kasashen duniya sun haramta amfani da su wadanda Amurka da Ingila ke ba Saudiyya da kawayenta suna amfani da su a Yemen.

A sauran yankunan kasar Yemen, akwai akalla yara 1,000 wadanda suka kamu da cutar kansar cikin jinin saboda wannan dalili.

Kungiyar ta Entisaf ta bayyana cewa akwai karancin magunguna domin yin maganin kansar saboda yakin na Saudiyyar da kulle bodar kasar, kuma yakin da kulle bodar ya hana yara marasa lafiya samun kulawa a kasar waje saboda matsin tattalin arzuki, inda suka yi rokon a bude babban filin jiragen sama na kasa-da-kasa da ke birnin Sana'a domin shigowa da kayan agaji.

Saudi Arabiya dai da wasu kawayenta daga cikin kasashen larabawa sun kaddamar da wani mummunan yaki ne a kan kasar Yemen a cikin watan Macin 2015 tare da samun taimakon kayan yaki da dabarun yaki daga kasar Amurka da wasu kasashen yamma.

Manufar kuwa itace a mukushe kungiyar Ansarullah wadda ke gudanar da al'amurran gwamnati bayan rasa wata takamaimiyar hukuma a kasar, tare da mayar da gwamnatin Abd Rabbuh Mansour Hadi wadda ta ke abokiyar Riyadh ce.

To saidai gamayyar ta kasa samun nasara a cikin dukkanin manufofinta, a yayin da a gefe daya dubunnan daruruwan mutanen Yemen suka rasa rayukansu, hakan kuwa ya haifar da daya daga cikin mummunan yanayi da wasu 'yan Adam suka samu kansu a duniya.

No comments

Powered by Blogger.