'Yan Nijeriya nawa ne suka kada kuri'a?
Sama da 'yan Nijeriya miliyan 87 ne suka yi rijistar zabe a Nijeriya, kuma tunda sassafe a ranar Asabar masu zaben suka fara fitowa domin tafiya runfunan zabensu domin zaben shugaban kasa da 'yan majalisu.
Mafi yawancin masu kada kuri'ar matasa ne kuma a wasu wuraren an sami jinkirin isowar malaman zabe da kuma matsalar na'urar tantance masu zabe ta BIVAS, to amma dai a wasu wuraren tuni aka fara kirga kuri'u.
Dukkan manyan 'yan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar NNPP da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour duk sun samu kada kuru'unsu.
A cikin wani jawabi da shugban hukumar zaben Nijeriya, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wa 'yan jaridu a kan zaben shugaban kasar da na 'yan majalisu, ya bayyana cewa sun samu labarin tayar da rikici a wasu mazabu a jihohin Borno, Legas da Bayelsa, amma lamarin ya daidaita.
Farfesa Mahmood ya bayyana cewa bayan samun matsala ta rasa saka alamar wata jam'iyya guda daya a cikin takardar kada kuri'a a wasu mazabu biyu a jihar Edo, ya sa an dage zaben sai ranar 11 ga watan Maris ranar gudanar da zaben gwamnoni da 'yan majalisu.
Ya bayyana cewa za a yi hakan ne saboda kowa doka ta ba shi damar yin zabe, saboda haka hukumar za ta kokarin ta wajen tabbatuwar hakan.
Kamar yadda ya bayyana, a ranar Lahadi za a bude karban sakamakon shugaban kasa na shekarar 2023.
Post a Comment