Header Ads

Yadda Shugaban APC ya caccaki Tinubu


Shugaban jam'iyya mai mulki ta APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana rashin jin dadin su bisa abin da dan takarar shugaban kasarsu, Ahmed Bola Tinubu, ya yi a garin Abekuta yayin gudanar da kamfe.

Sanatan ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi da gidan rediyon BBC, inda ya ce, "Mutumin da ake ganin girma da kimarsa a rayuwar jam'iyyarmu, bai kamata ba ko menene aka yi masa ya kawo maganar da ba ta shafi abin da ya kai shi ba. In wani ya muzanta masa ba shugaba Buhari ya muzanta masa ba, har ya kai ga yana fadin in ba domin shi ba, da gwamnatin nan ba ta samu ba. Yana fadin ba sau daya ba, ba biyu ko uku ba tsakanin Legas da Abuja shugaban kasa na bin sa ya ba shi goyon baya. Mutum mai hankali ba zai yi wannan maganar ba." 

Shugaban jam'iyyar ya shaidawa gidan rediyon cewa in da ya fito ya ce ba niyyar shi kenan ba muzantawa, to za a iya yarda, "Amma ko bugagge in ya yi abu irin wannan dama abin da ke cikin zuciyarsa ke nan. Ni kuma ba zan ce wannan dan taliki ba ya cikin hayyacin sa ba, ya je ne domin ya ga mutane domin ya bayyanar da abin da ke cikin zuciyarsa. Kuma wannan abu in muka bar shi haka ba zai yi dadi ba. 

"Kuma wannan shugaban namu Allah shi ya ba shi mulki, saboda haka duk wanda ya muzanta mutuncinsa ba za mu yarda ba."

Da yake amsa tambayar shin yadda ya fito ne jam'iyya ba ta yarda da shi ba ko kuwa alfarmar da ya ce ya yi wa shugaban kasa ne ake musanta hakan? Sai shugaban jam'iyyar ya ce, "Ban da rashin da'a, dauka ma cewa ya yi alfarmar, sai ya zo yana fada wa duniya? Mutunci ne hakan? Ai ba mutunci a nan, kuma dole ya san cewa bai yi daidai ba."

Dangane da bayyana cewa ba shi da burin da ya wuce ya mulki Nijeriya, amma ya lura akwai masu so su hana shi wannan da Tinubu ya yi, shugaban APC din ya ce ba wani ya sa shi yin abin da ya yi ba, kuma yana da damar neman shugaban kasa a matsayinsa na dan kasa, amma ba zai yi abin da babu kyau a sa ido ya ci gaba ba don yana neman shugaban kasa wai ko domin hakan zai bata tafiyarsa."

Shugaban Jam'iyyar ya bayyana cewa, sune gatan shugaba Buhari kuma sune APC, a karkashin jam'iyyarsu ya yi takara ya ci zabe, kuma duk wanda zai ci mutuncinsa ba za su yarda ba, ko waye shi.

No comments

Powered by Blogger.