Yadda Obi ya ka da Tinubu a Legas
An bayyana dan takarar kujerar shugban kasa a jam'iyyar LP (Labour Party), Peter Obi, a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa a jihar da ta fi kowacce yawan jama'a a Nijeriya, wato Legas.
Mista Obi dai ya samu kuri'u 582,454 ne a jihar, inda Ahmed Bola Tinubu na jam'iyyar APC ya samu 572,606 a yayin da Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya zo na uku da kuri'u 75,750.
Mutane 1,347,152 ne dai aka tantance domin gudanar da zabe a jihar
Kuri'u 1,335,729 aka kada a jihar, kuri'u 1,271,451 sune aka kada da kyau yayin da kuma wadanda suka lalace sune kuri'u 64,278.
Post a Comment