Header Ads

Tawagar tarayyar Turai da ta sa ido a zaben Nijeriya ta kalubalanci nagartarsa


Tawagar tarayyar turai da ta sa ido a zaben shugaban kasar da ya gudana a Nijeriya ranar Asabar, EU EOM, ta bayyana damuwa game da nagartar zaben da ya gudana. 

Tawagar, wadda ta bayyana haka ranar Litinin yayin wani taro a Abuja, ta ce an saba doka game da sirrinta takardun zabe a akasarin rumfunan zabe.

Kamar yadda tawagar ta fada a cikin rahoton ta, a rumfunan zabe 100 cikin 240 da hukumar ta sa ido ba ta tabbatar da sirrinta kuri'a ba kuma fiye da rabin masu kada kuri'u ba su sirrinta takardar jefa kuri'a ba.

Tawagar ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna takardar kuri'arsa domin nuna jam'iyyar da ya zaba a ranar zabe.

Game da matsalolin da aka fuskanta a wasu rumfunan kuwa da na'urar BVAS, tawagar ta ce ba a bi muhimman ka'idojin da aka gindaya ba a tsarin zaben.

Hukumar ta bayyana cewa kafin zaben, masu ruwa da tsaki sun bayyana gamsuwa da kwarewa ta hukumar zabe mai zaman kanta wajen wayar da kan masu zabe, amma an rasa duka wadannan a yayin da zabe ke gabatowa a Kano da Legas.

Tawagar ta bayyana cewa a rumfunan zabe 32 da aka sa ido, ba a yin wata alama a jikin rijistar sunayen masu zabe, kuma masu sa ido sun bayyana cewa an samu kananan yara da suka yi zabe a jihohin Kano da Sokoto.

Tawagar ta ce an samu sabanin alkaluma a wasu rumfunan zabe da tawagar ta sa ido.

Tawagar dai ta bayyana matsaloli da dama da aka fuskanta a yayin zaben.

Ita kuwa shugabar tawagar majalisar kasashen turai, Ms. Evin Incir, ta yi magana ne a kan karancin mata a mukamai, inda ta ce, "Ina so in bayyana rashin jin dadi na ganin cewa kasa da kashi 10 cikin 100 ne mata a cikin 'yan takarar. Gwamnati da majalisa mai zuwa yana da kyau su bi tsarin da manyan jam'iyyun Nijeriya suka tsara, wadanda ke nema a dauki mataki mai karfi, misali tsarin bayar da wani kaso (quotas)."

No comments

Powered by Blogger.