Su waye suka yi kutse a shafin A'isha Buhari?
Matar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta nuna barrantar ta da wasu sakonni da aka gani a shafukanta na sada zumunta na Facebook da Instagram, wadanda ke cewa babban bankin Nijeriya ya ba bankunan kasuwanci umarnin su cigaba da karbar tsofaffin naira 500 da 1,000.
Matar shugaban kasar, wadda ta dora laifin a kan batagari wadanda suka yi kutse a shafin na ta, ta ce tuni ta bayar da umarnin a goge su.
"An sanar da ni cewa an watsa wasu labarai na karya a shafukan sada zumunta na, Instagram wanda ya ke hade da shafina na Facebook a farkon safiyar nan. Tuni na bayar da umarnin a goge su.
"Wannan aikin wasu bata garin mutane ne wadanda suka goge min wasu sakonni tun cikin shekarar 2018 zuwa karshen shekarar da ta gabata lokacin da na watsa wani bidiyo tare da hotunan hannuwa na da ke da kunshi a ranar da na kaddamar da kwamitin mata na yi wa Bola Ahmed Tinubu kamfe a garin Ilorin da ke jihar Kwara, rubutuna kan al'amarin, wani a kan taron magungunan gargajiya (TCAM) da wasu har guda 17.
"Wannan mutum mai kutse ne, batagari wanda ke da niyyar bata mini suna ta hanyar shafukan sada zumunta na."
Rubutun dai na wannan karon na yin nuni ne da cewa matar shugaban kasar ta wallafa a shafinta wani jawabi na babban bankin Nijeriya cewa za a cigaba da karbar tsofaffin kudade har zuwa cikin watan Mayun shekarar 2023.
Tuni dai babban bankin Nijeriya ya yi watsi da wannan jawabi da aka wallafa.
Post a Comment