Header Ads

Shugaban Isra'ila ya yi gargadin kasar za ta iya "rushewa" a yayin da zanga-zanga ke kara ta'azzara a kasar

Shugaban kasar Isra'ila, Isaac Herzog, ya yi gargadin "rushewa" da "tarwatsewa" a yayin da zanga-zangar fusatattun 'yan Isra'ila ke kara ta'azzara a yankunan da aka mamaye kan shirye-shiryen 'yan majalisar da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ke jagoranta ke shirin yi na gyare-gyare ga tsarin shari'a a kasar. 

"Yanzu an dauki lokaci ba mu yi wata muhawara da ta shafi siyasa ba, amma muna gaf da fuskantar rushewar tsarin mulki da al'umma."

"Ina ji, muna ji dukkanmu, muna wani lokaci ne kafin wata arangama, babbar arangama. Hodar da ke cikin bindigar ta kusa tarwatsewa." 

Shugaban dai ya nemi majalisar wadda Netanyahu ke jagoranta da 'yan adawa su zauna zaman sulhu a cikin abinda ya kira "Wata rashin fahimta mai wahala."

Wadannan canje-canje suna so su samar da ikon siyasa a kan wadanda za a sa sashen shari'a ne da kuma rage karfin kotu a kan abinda majalisa ko dokoki Knesset suka tanada.

Wannan shiri dai gwamnatocin kasashen waje da yawa sun koka a kansa, cikin kuwa harda babbar kawar Tel Aviv, Amurka.

Sai dai hadakar da Netanyahu ke jagoranta na ikirarin cewa wannan canje-canje ana bukatar su domin, abinda ya kira, nuna iko da yawa na alkalai.

Jawabin na Herzog na zuwa ne kafin gudanar da muhawara a Knesset kan wadannan "canje-canje na doka." A yayin gudanar da muhawarar kuwa, dubunnan 'yan kasar sun taru a waje domin nuna kin amincewarsu da shirin.

Ana dai ta gudanar da zanga-zanga a kasar tun bayan da majalisar Netanyahu ta fara aiki a karshen watan Disamba.

A cikin shekarar 2019, Netanyahu ya kasance Firaminista na farko tarihin kasar da aka zarga da cin hanci yana a kan mulki. To amma ya ki sauka.

No comments

Powered by Blogger.