Header Ads

Shin da gaske CBN ya umurci bankuna su ci gaba da karɓar tsofaffin naira 1,000 da 500?


Babban Bankin Najeriya ya umurci bankuna su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin naira 1,000 da 500 waɗanda yawansu bai zarta N500,000 ba.

Bankin na CBN ya bayyana haka ne a yau Juma’a, bayan koke-koken da ake ta samu a faɗin ƙasar kan wahalar da al’umma ke fuskanta wajen samun sababbin kuɗin.

Mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi ya tabbatar wa BBC da wannan bayani.

Sai dai a lokacin da yake tabbatar wa BBC da matakin, Mr Nwanisobi bai tantance ko akwai wani wa’adi na karbar kudin ba ko a’a.
Haka nan bai yi karin bayani kan dalilan da suka sanya CBN din ya dauki matakin ba.

Rahotanni daga wasu jihohin Najeriya dai sun bayyana cewa an gudanar da zanga-zanga kan ƙarancin sababbin kuɗin.

An buƙaci jama'a su kai tsofaffin takardun kuɗinsu zuwa bankuna domin a musanya musu su da kwatankwacin kuɗin amma sababbi, sai dai tun gabanin wannan lokacin babban bankin Najeriya ya yi hani ga 'yan Najeriya su riƙa cirar kuɗin da ya zarce naira 100,000 zuwa naira 500,000 a kowane mako ga kowane ɗan ƙasar ko ga kamfanoni.

A ranar Alhamis ne shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga al'ummar ƙasar, inda ya bayyana tsawaita amfani da tsofaffin takardun kuɗi na N200.

Sai dai duk da hakan wasu jihohin sun buƙaci al'umma su ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗaɗen na naira 1,000 da 500 da kuma 200.

Dama dai kotun ƙolin ƙasar ta ta buƙaci a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin har sai lokacin da ta yanke hukunci bayan ƙarar da wasu gwamnonin jihohin ƙasar suka shigara a gabanta.

No comments

Powered by Blogger.