Shin Buhari ya saba dokar zabe yayin jefa kuri'a?
Ko nuna kuri'ar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a Daura ya saɓa wa dokokin Najeriya?
Masana dokoki na tsokaci kan yadda shugaba Buhari ya nuna jam'iyyar da ya zaba a bainar jama'a.
Barrister Amina Umar na ganin hakan ya sha bamban da dokokin zaɓe.
Ta ce a dokar zabe sashe na 50, karamin sashe na daya cewa ya yi a yi zaɓe mai tsarin "open secret ballot," wato a sarari mai zaɓe zai jefa kuri'a, ba tare da an san abin da ya zaba ba.
Barista Amina ta ce hikimar yin wannan doka ita ce kar wani ya yi tasiri a kan ra'ayin wani mai kada kuri'a a wurin zaɓen.
Don haka akwai yiwuwar yadda Buhari ya nuna cewa APC ya dangwala wa kuri'arsa, ta sa wasu da dama sun yi koyi da shi.
Wata tambayar da ya kamata Lauyoyi su ba da amsar ta ita ce, shin akwai hukuncin da za a yi wa wanda ya yi irin abin da Buhari ya yi a lokacin zaben nan?
Me ke ra'ayinku?
Post a Comment