Header Ads

Sheikh Shuraim ya yi murabus daga limancin masallacin Makka

Shaikh Shuraim

Limamin din-din-din na masallacin Makka, Sheikh Saud Ash Shuraim ya ajiye aikin limancin masallacin.

Cikin wata sanarwa da shafin Haramain Sharifain ya fitar a shafinsa na sada zumunta, ya ce Shuraim ya yi murabus ɗin ne bayan shafe shekaru 32 yana gudanar da aikin limanci. An dai nada shi Liman ne a 1412H.

Imam Shuraim ya ce wasu dalilansa na kashin kai ne suka sanya shi ajiye maƙamin shugabancin limanci.

Zai iya komawa ya ci gaba da jagorancin sallar tarawihi a matsayin baƙon limami, wanda za a sanar da dalilan haka nan da makonni masu zuwa.

No comments

Powered by Blogger.