Header Ads

Shaikh Isa Qassim ya gargadi Sarkin Bahrain kan daidaita alaka da Isra'ila

Ayatollah Shaikh Isa Qassim

Sanannen malami da ke kasar Bahrain, Ayatollah Sheikh Isa Qassim, ya gargadi wasu kasashen larabawa a kan daidaita alaka da Isra'ila, inda ya ce hakan ba bai yi daidai da taimakon yunkurin Falasdinawa ba, hatsari ne ga tsaro, albarkatu da tsarkin duniyar musulunci.

Sheikh Qassim ya bayyana adawa da hakan da abu ne da yake tabbatacce, inda ya ce, "Idan har labarin mayar da kasar Bahrain wani dandali na Isra'ila ya tabbata a tsakanin kasashen yankin tekun Gulf, ko kuma aka yi wani yunkuri domin tabbatar da hakan, to wadanda suka kirkiro wannan al'amari za su gamu da rashin amincewa daga mutanen kasar Bahrain, mun gode Allah saboda tsayuwarsu kyam kan addini, ba za su bari wannan manufa ta tabbata ba."

"Mahukunta a Bahrain suna tunanin za su cigaba da kasancewa a kan mulki ne idan sun daidaita wannan alakar tare da cigaba da kama malamai da manyan mutane suna kullewa a cikin kurkuku, wannan kuwa shi ke kara nuna cewa kin amincewa da wannan ra'ayin nasu ya zama wajibi."

"Al'amarin Falasdinawa zai cigaba da kasancewa wani babban al'amari ga daukacin larabawa da duniyar musulunci. Daidaita alakar diflomasiyyar ba karamin hatsari yake da shi ba kuma bai yi daidai da yunkurin Falasdinawa ba. Domin haka nuna goyon baya ba tare da gajiyawa ba ga Falasdinawa zai kawo karshen makirce-makircen wadanda ke yunkurin daidaita alakar da Isra'ila da masu goyon bayansu." Kamar yadda shehin malamin ya bayyana.

A yayin da ake cigaba da nuna adawa da yunkurin daidaita alaka da Isra'ila, kasar Bahrain ta aike da manyan jami'an tsaron ta kasar a wuraren da aka mamaye domin kara karfin dangantaka da Isra'ila duk da cewa mutanen kasar ba su aminta ba.

A cikin dai watan Satumbar 2021 ne kasar Bahrain da masarautar Hadaddiyar Daular Larabawa suka sanya hannu wajen daidaita alaka da Isra'ila yayin wani taro a birnin Washington da goyon bayan kasar Amurka.

Kasashen Sudan da Morocco su ma suka biyu baya a shekarar 2022 wajen daidaita alakar ta diflomasiyya da goyon bayan kasar ta Amurka.

No comments

Powered by Blogger.