Header Ads

Sama da mutane 7,500 sun rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa mai karfin gaske a kasashen Turkiyya da Syria

Masu aikin ceton rai a Turkiyya

Wata girgizar kasa mai karfin 7.8 ta afku a kasashen Turkiyya da Syria, inda ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane sama da 7,500 tare da danne wasu da dama a karkashin gine-gine.

Girgizar kasar ta afku ne da karfe 4:17 na safe wadda ke da tsawon kilomta 17.9 sai kuma wata girgizar kasar mai karfin 6.7 ta biyo bayanta bayan mintuna 15, kamar yadda US Geological Survey suka bayyana.

Cibiyar taimakon gaggawa ta kasar Turkiyya ta sa karfin girgizar kasar a kan mataki na 7.4, a yayin da shi kuma mataimakin shugaban kasar ta Turkiyya, Fuat Oktay, a cikin jawabinsa ya bayyana cewa mutane 7,284 suka rasa rayukansu kuma sama da 12,300 suka jikkata, mafi yawancin rahoton rasuwar kuma daga yankin kudancin Kahramanmaras ne ya fito inda nan ne cibiyar girgizar kasar.


Wannan girgizar kasa dai ta rushe gine-gine da dama a manyan biranen kudancin Turkiyya wadanda suka hada da Kahramanmaras da Gaziantep a Syria kuwa a garuruwan Aleppo, Hama da wasu yankuna na kusa.

Kamar yadda wani jami'in lafiya ya shaida, mutane sama da 4230 suka rasa rayukansu a yayin da wasu sama da 5600 kuma suka jikkata, mafi yawansu daga garuruwan Aleppo, Hama da Latakia.

Tuni dai shugaban kasar Syria, Bashar Asad ya kira taron gaggawa da 'yan majalisarsa domin tattauna yawan barnar da lamarin ya haifar tare da tattauna menene mafita, kamar yadda ofishinsa ya sanar.

Girgizar kasar, wadda an jiyo ta daga kasashen Lebanon da Cyprus, Raed Ahmed, shugaban cibiyar kula da girgizar kasa ta kasar Syria ya bayyanawa Syria Media cewa wannan itace girgizar kasa mafi karfi da cibiyarsu ta taba gani.


Kasar Turkiyya ta kasance daya daga cikin cibiyoyin girgizar kasa a duniya, a shekarar 1999, sama da mutane 17,000 suka rasa rayukansu sakamakon wata babbar girgizar kasa da ta faru a cikin shekaru dama a kasar.

No comments

Powered by Blogger.