Header Ads

Sabuwar naira: 'Yan Nijeriya ba za su samu sabbin kudi ba har sai bayan zabe saboda wata boyayyar manufa - Fani - Kayode

Femi Fani Kayode

Darakta mai kula da bangaren yada labarai na kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Tinubu da Shettima, Femi Fani - Kayode, ya bayyana cewa 'yan Nijeriya ba za su samu sabbin kudi ba har sai bayan babban zaben shekarar 2023 da ke tafe, saboda abinda ya kira da "wata boyayyar manufa."

Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ya ke tattaunawa da gidan talabijin din Channels Television a cikin shirin su na Politics Today a ranar Laraba.

"Zai yi wahala mutane su samu sababbin kudaden saboda akwai wata boyayyar manufa." Kamar yadda ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.