Header Ads

Sabuwar Naira: Hadakar kungiyar shugabannin matasan kudu maso gabas sun koka kan karancin sabbin kudi

Hadakar kungiyar shugabannin matasan kudu maso gabas (COSEYL) sun yi kira ga babban bankin Nijeriya da ya tabbatar da cewa sababbin naira sun yawaita a cikin kwanaki goma da ya kara.

A yayin da yake bayani a cikin wata takarda da suka fitar a ranar Talata, sakataren kungiyar, Goodluck Ibem, ya yi kira ga bankin da ya tabbatar da ya saki sababbin kudaden domin 'yan Nijeriya su iya yin kasuwancinsu yadda ya kamata.

"Rashin sababbin kudaden sun sa hada-hadar kasuwanci da dama tsayawa a cikin kwanakin baya" kamar yadda ya ke a cikin takardar.

A dai ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban babban bankin na Nijeriya, Godwin Emefiele, ya kara wa'adin canjin kudin zuwa 10 ga watan Fabrairun wannan shekara bayan da ya je Daura ya gana da shugaba Muhammadu Buhari.

No comments

Powered by Blogger.