Header Ads

Sabbin Naira: Ko Gwamnonin APC za su iya shawo kan Buhari?

Gwwmnonin APC a Villa 

Gwamnonin da ke mulki a karkashin jam'iyyar APC a Nijeriya sun nemi Buhari da ya bari a yi amfani da sabbin kudade da kuma tsofaffi a tare.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana hakan ga 'yan jaridu bayan tattaunawar da suka yi da shugaban kasar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamnan ya bayyana cewa a yayin da babban bankin na Nijeriya ya ke ruke da sama da naira tiriliyan biyu na tsofaffin kudi da ya karba, naira biliyan 300 kawai ya buga wanda kuma ba su isa ba.

El-Rufai, wanda ke jawabi tare da takwaransa gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa kamata ya yi babban bankin ya buga akalla naira tiriliyan 1, rabin abinda ya maido sannan sai a yi tsarin na rashin kudade a hannu (cashless policy).

El-Rufai wanda ya ce sun shaidawa shugaban kasar cewa mutane na shan wahala, ya ce shugaban kasar bai amsa masu da ya yarda ko bai yarda ba.

To saidai gwamna Ganduje ya ce shugaban kasar ya ce zai yi duba cikin al'amarin.

No comments

Powered by Blogger.