Header Ads

Sabbin Naira: Gwamnan Borno ya yi gargadi ga bankuna


Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, yayin wata ziyara da ya kai bankuna domin ganewa idanunsa irin dogayen layuka da wahalhalun da jama'a ke sha wajen samun sabbin kudi, ya gargadi bankunan da ke kasuwanci a jiharsa cewa zai kwace lasisin filayen duk bankin da ya gaza saka sabbin takardun naira a na'urar cire kudi ta ATM.

Gwamnan, wanda ya yi gargadin a ranar Juma'a a birnin Maiduguri, ya bayyana cewa "Duk bankin da ba shi da niyyar cika ATM dinsa da sababbin takardun kudi domin saukakawa jama'a wahalhalun da suke ciki za mu kwace filin gininsa nan take." Kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa, Isa Gusau, ya fitar ta bayyana.

Sanarwar ta bayyana cewa ran gwamnan ya baci a yayin da ya ga wani dogon layin cirar kudi, inda na'urar ATM daya ce kawai ke aiki cikin na'urori goma da ke wajen.

Gwamnan ya bayyana cewa a karamar hukumar Gubio da ya je, ya tarar da cewa babu N100,000 gaba daya a karamar hukumar na sabbin kudaden ko tsofaffi.

"Kamar yadda kuke gani, talakawa ne kawai a kan layi, an ce wasu tun karfe 3:00 na dare suke nan, wasu ma ba su ci komai ba. Sababbin kudin da tsofaffi duka babu, wanda hakan ke shawar harkokin kasuwanci da kuntatawa mutane." Kamar yadda gwamnan ya bayyana.

A fadin Nijeriya dai karancin kudin na cigaba da jefe mutane cikin wahalhalu, inda mutane da dama ke kwashe awanni a kan dogayen layuka domin cire kudadensu.

No comments

Powered by Blogger.