Header Ads

Rashin magunguna a Yemen na barazana ga rayuwar mutane sama da 5,000 masu ciwon koda

Wani majinyaci Bayamane

Ma'aikatar lafiya ta kasar Yemen ta yi gargadin cewa sama da mutane 5,000 masu fama da ciwon koda na cikin barazanar rasa rayukansu dalilin rashin magunguna sakamakon yakin shekaru na Saudiyya da kulle bodojin kasar ta larabawa.

Kakakin ma'aikatar, Anis al-Asbahi, ne ya yi wannan gargadin a yayin da ya ke tattaunawa da kafar watsa labarai da harshen Arabiya na kasar Rasha, Sputnik news agency, a ranar Asabar a yayin da yakin da Saudiyya ke jagoranta tare da kulle tashar jirgin ruwan kasar ya cigaba tsawon shekaru takwas.

"Magunguna da sauran kayan tace jini (dialysis) sun karanta, ba mu da isassun kaya a cibiyoyin tace jini, wadanda suka rage watan Maci kawai za su kai." Kakakin ya bayyana, inda ya kara da cewa in har ba su samu an kawo masu magunguna cikin gaggawa ta jirgin ruwa a wannan wata da ake ciki ba, to za a fuskanci wani "ibtila'i" ne wanda zai jefa rayuwar masu ciwon koda da ke bukatar a tace jininsu sama da 5,000 cikin hadari tare da kuma wasu 5,00 da ke bukatar a canza masu koda.

Asbahi, wanda ya bayyana cewa cibiyoyin tace jinin masu ciwon kodar 17 za a kulle su in har ba a kawo magungunan da wuri ba, ya kalubalanci hukumar lafiya ta duniya (WHO) saboda daukar tsawon shekara daya kafin su kawo magani duk kuwa da cewa sun san halin da ake ciki.

Kakakin ya dora laifi kan kungiyar lafiya ta duniya sakamakon rashin yin gaggawa da daukar mataki duk kuwa da cewa sun san irin hatsarin da kulle bodoji, kulle tashar jiragen sama na kasa-da-kasa da ke Sana'a da kuma matsin tattalin arzuki da kasar ke ciki.

Asbahi ya zargi majalisar dinkin duniya da hukumar lafiyar ta duniya da "kara wahalhalun" da masu ciwon kodar ke ciki ta hanyar nuna ko in kula da nuna rashin sanin halin da suke ciki.

Jami'an lafiyar kasar Yemen a wurare da dama sun sha nuna muhimmancin bude tashar jiragen saman da ke birnin Sana'a da tashar jirgin ruwa da ke Hodeidah domin kuwa hanyoyi ne muhimmai wadanda za a iya shigo da abinci da magunguna ga miliyoyin jama'ar kasar Yemen da ke cikin wahalar yaki da kawance karkashin jagorancin Saudiyya ke yi.

Ko a farkon watan nan, wata kungiya mai fafutikar kare hakkin mata da yara, Entisaf, ta bayyana cewa sama da yara 3000 wadanda suka samu cutar kansa sakamakon yakin da Saudiyyar ke jagoranta tare da kulle bodojin sama, kasa da ruwa na kasar, na cikin hatsarin rasa rayukansu.

Kungiyar ta kalubalanci majalisar ta duniya da sauran manyan zauruka na duniya da nuna rashin kulawa ga marasa lafiyan masu fama da kansa.

Wannan yaki dai, wanda Saudiyya ke jagoranta tun watan Macin shekarar 2015 tare da taimakon kasar Amurka da wasu kasashen yamma, ya kasa cimma kowacce manufa tashi a yayin da dubunnan daruruwan 'yan kasar Yemen suka rasa rayukansu.

No comments

Powered by Blogger.