Header Ads

Minista a Isra'ila ya ba da umurnin nunka yawan Yahudawa masu rike da bindigogi

Minista Itamar Ben-Gvir

Wani minista a Isra'ila, Itamar Ben-Gvir, ya ba da umarnin nunka yawan wadanda ake ba lasisin rike bindigogi mazauna Isra'ila a yayin da sojojin mamayar na Isra'ila ke cigaba da kashe Falasdinawa a hare-hare da dama a yankin yamma da kogin Jordan.

Ministan, wanda ya ke cikin masu bayar da shawara a bangaren tsaro, ya bayar da umarnin nunka wadanda ake ba damar rike bindigogi daga mutum 2,000 zuwa mutum 10,000 a cikin wata daya, kamar yadda jam'iyyarsa ya Otzma Yehudit Party ta bayyana. 

Ba dai abin mamaki ba ne a ga mazauna 'yan Isra'ila rike da kananan bindigogi ko kuma sojojin da ba ma suna kan aiki bane dauke da makamai a yankunan da suka mamaye, to sai dai akwai yiwuwar wannan umarni ya kara sa tsoron hauhawar yawan hare-hare ga Falasdinawa.

Jami'in kare hakkin bil-adama na majalisar dinkin duniya, Volker Turk, ya yi gargadin cewa wannan shirin na kara yawan bindigogi a hannun fararen hula zai kara yawan rikice-rikice ne kawai da shekar da jini.

Sojojin Isra'ila dai sun kara yawan hare-haren su a garuruwan Falasdinawa a cikin watannin baya-bayan nan a kokarinsu na hana yunkurin Falasdinawa a yankunan da suka mamaye, inda Falasdinawa da dama suka rasa rayukansu. A cikin watan Janairun shekarar 2023 kawai, Falasdinawa akalla 38, cikin su har da yara biyar, suka kashe.

Wannan umarni na zuwa ne a yayin da dama Ben-Gvir yake da tarihi sananne wajen tunzuruwa a musgunawa Falasdinawa.

Akwai lokacin da ya dauko bindiga mai cike da harsasai yana nunawa a yankin gabashin al-Quds da aka mamaye a Sheikh Jarrah a cikin tsakiyar watan Oktobar shekarar 2022, yana fadin, "Mu ne masu gidaje a nan, kun tuna da haka? Ni ke da mallakin muhallanku." Sai kuma ya umarci mazauna wajen da su bude wuta ga Falasdinawa da ke jefo duwatsu domin kare kansu daga mamaya.

A cikin farkon watan da ya gabata ma ya yi barazana ga Falasdinawa da suke yunkurin mayar da martani ga sojojin Isra'ila da mazauna yankunan da Isra'ilan ta mamaye da sanya su a "Kujerun wutar lantarki."

No comments

Powered by Blogger.