Header Ads

Me ya sa sojoji suka kashe Tijjanawa a Burkina Faso?

Daya daga cikin waɗanda aka kashe
A ranar Laraba 1 ga watan Janairun shekarar 2023 ne aka samu labarin rasuwar Tijjanawa matafiya kasar Senegal domin kai ziyara ga Maulana Sheikh Ibrahim Inyass. 

Wannan tawaga dai ta hadu ne da sojojin kasar Burkina Faso wadanda suka fito dasu daga cikin motocinsu suna zargin cewa 'yan ta'adda ne kuma suka bude masu wuta har lahira.

Hanyar da matafiyan suka biyo, wadda ake kira hanyar Kancare, hanya ce mara kyau wadda mutane tun kusan shekaru biyar suka daina bin ta saboda yadda 'yan ta'adda suka mayar da ita sansaninsu. 

Daya daga cikin matafiyan ya bayyana cewa tun a kan iyakar Nijar da Burkina Faso, sojoin kan iyaka suka shaida masu cewa akwai 'yan uwansu ma'aikata da ke tahowa daga wani waje kuma sojoji ne masu hadarin gaske.

To amma duk da wannan bayanin ba su tsaya ba suka cigaba da tafiya, kuma kamar yadda ya bayyana suna cikin tafiya sai suka hadu da wannan runduna wadda akalla ta kai ta sojoji mutum dari biyar, kuma nan take suka tsayar da motocinsu suka fara bincike, suna sauke masu kama da Fulani da kuma wadanda suka tara gashi mai yawa a kansu suna harbewa, kamar yadda ya bayyana, sun harbe jumullar mutane goma sha tara.

Matafiyin sai ya yi kira ga jakadan Nijeriya a kasar Burkina Faso, Mister Marc Bassey Egbe, da ya gaggauta sanar da hukumar kasar abinda ya faru na kisan gillar da sojojin kasar suka yiwa 'yan asalin kasar ta Nijeriya.

Ya kuma kara da cewa suna kira da babbar murya ga ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje da lallai su binciki wannan al'amari mai cike da rashin imani da rashin tausayi wanda wadannan sojoji suka aikata a kan wadannan bayin Allah, bayan, kammala bincikensu kuma su hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da biyan iyalan mamatan diyya.

Sai kuma matafiyin ya yi fatar Allah ya karbi shahadar matafiyan albarkar Manson Rahama (S).

No comments

Powered by Blogger.