Kasar Iran za ta karrama wanda ya farmaki Salman Rushdie
Jamhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa za ta karrama Hadi Matar, wanda ya ke dan shekara 24 a watan Agustar shekarar 2022, da wani babban filin noma mai fadin mita 1,000 sakamakon hari da ya kaiwa marubucin da ya yi batanci ga al-Kur'ani, Salman Rushdie.
Salman Rushdie, wanda marubuci ne dan kasar Ingila, ya yi batanci ne ga al-kur'ani a cikin wani littafi da ya rubuta.
Mohammad Ismail Zarei, shugaban sakatariyar tabbatar da zartar da fatawar Imam Khomeini ta hukuncin kisa a kan Salman Rushdie, a ranar Litinin ya bayyana cewa, "Muna matukar mika godiyar mu ga matashin dan Amurka a kan jarumtakar da ya nuna wajen tabbatar da fatawar Imam Khomeini mai dadadden tarihi."
Hadi Matar ya sari Salman Rushdie ne a wuya da jikinsa a yayin da ya ke gaban wani taro yayin wata lakca da aka gudanar a jihar New York, sakamakon hakan wanda ya yi batancin ya rasa ido daya kuma baya iya motsa hannunsa daya bayan wata doguwar kulawar likitoci da ya samu.
"Wannan abin da ya yi ya sa idon Salman daya ba ya aiki kuma kafadarsa daya ba ta aiki domin ya faranta ran musulmai." Sakataren ya bayyana.
"Duk da cewa yanzu Salman ba wani abu ba ne illa gawa mai tafiya, domin a karrama wannan jarumta da wanda ya yi sarar ya yi, za a karrama shi da kasar noma mai kyau mai kusan mita 1,000 ko kuma wakilinsa na hakika a wani biki da za a yi."
Sai ya kara da cewa sauran filin kasar noman za a mika ta ne ga wadanda suka kashe Salman Rushdie.
Mutane da yawa suna zargin cewa Iran na da alaka da matashin, sai dai Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Iran ta musanta cewa akwai wata alaka da matashin mai shekaru 24. Mutane da yawa dai sun nuna farin cikinsu bayan kai harin.
Post a Comment