Header Ads

Kamata ya yi Nijeriya ta yanke albashin masu rike da ofisoshin siyasa sakamakon bashin tiriliyan 44 da ake bin ta - 'Yar takarar jam'iyyar NNPP

Princess Helen Mbakwe
Wata mai neman kujerar sanata a karkashin jam'iyyar NNPP daga yankin jihar Anambara ta tsakiya, 
Princess Helen Mbakwe, ta koka akan tsadar tafiyar da al'amurran gwamnati.

Helen, wadda ta ke jawabi yayin wata tattaunawa da aka yi tsakanin mambobin kungiyar 'yan jaridu ta NUJ da majalisar jihar ta Anambara, ta ce abin takaici ne a ce kasar da ake bin ta bashin tiriliyan 44, amma kashe kudaden gwamnati na cigaba ba cikakkiyar kula.

Ta dai bayyana cewa abinda ya fi ga kasa kamar Nijeriya mai fama da matsalar bashi shine ta rage kudaden gudanarwar gwamnati da yanke albashi da sauran kudade daban-daban na masu ruke da ofishoshin siyasa.

'Yar takarar wadda ke jawabin a dakin taro na Godwin Ezeemo International Press Center da ke Awka, ta bayyana cewa, "Kasar da ake bi bashin sama da naira tiriliyan 44 ba ta da wani dalilin da zai sa ta runka almubazararanci a wajen kashe kudade da sawo kayayyaki, ba tare da kokarin yin tanadi domin gudanar da ayyuka ba." 

'Yar takarar ta bayyana cewa 'yan siyasa da ke neman a sake zaben su a majalisun kasa suna da son ofishin ne kawai amma a tunaninta shekaru 4 sun isa dan siyasa na kwarai ya cimma manufofinsa ya kuma mika mulki ga wani mai sabbin dabaru ko manufofi.

Ta ce a matsayin ta na 'yar majalisa ba wai kawai za ta tabbatar da cewa manufofinta sun wanzu ba ne, amma za ma ta tabbatar da cewa ta jawo ra'ayin cibiyoyi, hukumomin gwamnati da sauran kungiyoyi wadanda za su taimaka wajen tabbatuwarsu domin cigaban yankin Anambara ta tsakiya da Nijeriya baki daya.

No comments

Powered by Blogger.