Header Ads

Kalaman El-Rufai babu dattijantaka da girma a ciki - Bafarawa


Tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma jigo a jam'iyyar PDP, Alhaji Attihiru Bafarawa, ya mayar da martani ga wasu kalamai da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya yi a cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC, inda tsohon gwamnan ya bayyana cewa babu dattijantaka cikin kalaman gwamnan.

Shi dai gwamnan na Kaduna a cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC kan zargin da suke akwai masu yiwa jam'iyya zagon kasa da ke fakewa da zancen canza takardun kudi domin ganin sun fadi zabe, ya bayyana cewa, "Batun wani dattawa babu wani dattawa, ni ma dattijo ne domin a wannan shekarar ta 2023 zan cika shekaru 63, don haka su waye dattawan arewa, mu gwamnonin arewa mu ne dattawan arewa, kuma mu ne shugabannin arewa." 

Tsohon gwamnan dai ya bayyana wadannan kalamai da cewa cin fuska ne kuma akwai rashin dacewa a ce El-Rufai ya yi jam'i, domin na kirki ba sa karewa.

Attahiru Bafarawa ya kara da cewa ai shekaru ba sune dattako ba, domin akwai masu karancin shekaru amma tunaninsu na manya ne da sanin ya kamata.

"Sannan da ya ke magana shekarunsa 63, sannan ba ya ganin da sauran dattijai a arewa, to mu muna ganin wadannan maganganu akwai rashin dattijantaka a cikinsu.

"Kalaman El-Rufai babu dattijantaka da girma a ciki, saboda kalaman da ya kamata ya yi shi ne kalaman cigaban arewa, da cigaban kasa da jama'a baki daya."

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa da El-Rufai ke cewa sun gama cin zabe, sai Tinubu ya ci zabe, wa ya fada masa duk arewa APC ake yi? "Yadda ya ke yiwa Tinubu kamfe, muma muna yi wa dan takararmu."

Attihiru Bafarawa, wanda ya bayyana cewa mutum ba shi da ikon cusawa mutane dan takararsa, ya bayyana cewa, "Za mu ba su mamaki, domin sai mun nuna masu cewa kasar nan ba ta kowa bace, hakazalika arewa."

No comments

Powered by Blogger.