Header Ads

Ka fuskanci shari'ar da ke zagaye da tsige ka daga sarauta - Gwamna Ortom ya kalubalanci Sanusi

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi
Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya kalubalanci tsohon sarkin jihar Kano, Sanusi Lamido Sanusi, da ya mai da hankali ne a kan shari'ar tsige shi daga karagar mulki.

A cikin wata takarda wadda aka rabawa manema labaru, mai magana da yawun gwamnan, Nathaniel Ikyur, ya ce gwamnan ya fadi hakan ne a asibitin jami'ar Benuwe yayin kaddamar da wata cibiya mai suna DOHAPITU Clinic.

"Tsohon sarkin na Kano a cikin wani bidiyo da ya yadu sosai ya yi kokarin danganta sunan gwamnan jihar Benuwe, Samual Ortom, da wani al'amarin ban takaici da ya faru a jihar Nasarawa, inda aka yi ikirarin cewa wasu Fulani makiyaya sun rasa rayukansu sakamakon harin jirgin sama. Wannan al'amari kuwa har yanzu hukuma na kan gudanar da bincike a kansa.

"A cikin wannan bidiyo kamar sauran bidiyoyi, ana kokarin bata sunan gwamna Ortom ne a wajen kabilar Fulani, tsohon sarkin ya yi kira ga gwamnan da ya yi koyi da 'yan uwansa gwamnoni wajen iya kula da al'ummu daban-daban, inda ya nuna  gwamnan Filato a matsayin misali," kamar yadda takardar ta kunsa.

To sai dai gwamnan ya yi kira ga tsohon sarkin na Kano, Sanusi Lamido Sanusi, da ya gujewa shiga harkokin jihar Benuwe, kuma gwamnati ko gwamnan jihar Benuee ba su da ikon tura jirgi mara matuki ko jirgin yaki ko'ina a Nijeriya.

Gwamnan ya kara da cewa dokar hana kiwo a ko'ina wadda tsohon sarkin ke adawa da ita ba ta ci karo da tsarin mulkin Nijeriya ba, inda ya ce ya yi mamaki yadda tsohon sarkin ke shawartar sa ya mulki jama'ar Benuwe kamar yadda gwamnan Filato ke mulkar mutanensa, domin kuwa shi mutanen Benuwe ne suka zabe shi kuma su zai kula da bukatunsu ba na wani mutum a Kano ba.

No comments

Powered by Blogger.