Header Ads

Jami'an tsaro za su kare rayuka da lafiyar malaman jami'o'in da za su yi aikin zaɓe - INEC

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban INEC (dama)

Daidai saura makonni biyu a gudanar da zaɓe, Shugaban Hukumar Zaɓe na Ƙasa Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar wa Shugabannin Jami'o'i cewa za a kare rayuka da lafiyar dukkan malaman da za su yi aikin zaɓe.

Yakubu ya ce INEC na aiki tare da dukkan ɓangarorin jami'an tsaro na faɗin ƙasar nan domin samar da cikakken tsaro ga ma'aikatan da za su yi aikin zaɓe a matakai daban-daban har matakai 10.

Daga saman jerin sunayen muƙaman masu aikin zaɓe akwai Babban Baturen Zaɓe na Jiha, Jami'an Tattara Sakamakon Zaɓe na Jihohi, Baturen Zaɓe da Mataimakin sa da kuma masu sa-idon da aka tantance yardar su kula da yadda ake gudanar da zaɓen. Akwai kuma 'yan jarida, waɗanda su ma waɗanda aka tantance ne za su riƙa zagayawa ɗauko labaran abin da ke faruwa a rumfunan zaɓe da cibiyoyin tattara sakamakon zaɓen.

Shugaban INEC ya ce an tanadi inshora ga duk wani ma'aikacin da aka tantance zai yi aikin zaɓe.

Shugabannin jami'o'i sun nuna wa Shugaban INEC abubuwan da su ke da damuwa a kai, a lokacin ganawar ta su a Hedikwatar Hukumar Jami'o'i ta Ƙasa, wadda ke kusa da Hedikwatar INEC a Abuja, a ranar Alhamis.

Yakubu ne dai ya nemi a yi ganawar domin nan amincewa a ɗauki sunayen malaman jami'o'i da za su yi aikin zaɓe.

Sai dai wasu shugabannin jami'o'in sun nuna ɗar-ɗar dangane da matsalar tsaro a wasu yankunan da za a tura wasu malaman a wuraren da ba cikin birane ba.
A nan, Yakubu ya tabbatar masu da cewa a ko'ina har a cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.

Ya ce ya gana da shugabannin ɓangarorin tsaro na ƙasar nan, kuma sun tabbatar masa da cewa za su samar da isasshen tsaro.

"Za mu yi aiki ne tare da ma'aikatan tsaro, kuma sun tabbatar min cewa za su samar da isasshen tsaro.

Yakubu ya ce za a fara horas da malaman jami'o'i aikin zaɓe a ranakun 21 da 22 ga Fabrairu.

No comments

Powered by Blogger.