Isra'ila ta kai hare-hare ta jiragen sama a Gaza bayan ta yi kisan kiyashi a Nablus
Isra'ila ta kai hare-hare ta jiragen sama a Gaza kwana daya bayan sojojin mamayar sun yi mummunar barna a birnin Nablus da ke yamma da gabar kogin Jordan.
A ranar Alhamis jiragen saman Isra'ila suka kai hare-hare ta sama a arewacin birnin Gaza, hakan ya sa hayaki ya cika sararin samaniya a daya daga cikin wuraren da suka hara.
Wadannan hare-hare na zuwa ne awowi bayan sojojin Isra'ilan sun yi ikirarin cewa Falasdinawa masu fafutika sun harba rokoki shida cikin Isra'ila a garuruwan kusa da ruwa na Sderot da Ashkelon da yamma, inda aka jiwo karar jiniyar gargadi a garuruwan, tare da bayyana cewa biyar daga cikin rokoki an kabar da su, daya ya fada a wani fili, ba kuma su sanar da hakan ya haifar da rauni ko lalata wani wuri ba.
Wasu wadanda abin ya faru a idonsu Falasdinawa, sun ce akalla rokoki takwas aka harba.
Harba rokokin dai kamar ramuwar gayya ne sakamakon mummunar barna da Isra'ila ta yi Nablus kwana daya kafin nan, akalla Falasdinawa 11 ne suka rasu.
A barnar da Isra'ilan ta yi a Nablus, sama da Falasdinawa 100 suka raunata, cikinsu har da wani mutum dan shekara 72, wani yaro dan shekara 14 da kuma kwamandoji guda biyu na kungiyar fafutikar Falasdinawa da ke Gaza ta Islamic Jihad.
Babban sakataren kungiyar fafutika ta Islamic Jihad, Ziad al-Nakhala, ya bayyana barnar da "babban laifi" inda ya ce Falasdinawa ba za su bari wadannan zalunce-zalunce su kasance ba hukunci ba.
Falasdinawa dai 61, cikinsu wasu da bindigogi wasu fararen hula, aka kashe a cikin wannan shekarar ta 2023, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta bayyana.
Post a Comment