Header Ads

Islamic Center da ke kasar Italiya ta wallafa littafi kan Laftanar Janar Qassem SoleimaniIslamic Center da ke kasar Italiya ta wallafa littafi a kan rayuwar kwamandan kasar Iran, marigayi Laftanar Janar Qassem Soleimani, mai suna "A God's Fighter."

Littafin na magana ne a kan dagewar Janar Soleimani wajen samar da kariya ga mutanen da ake cutarwa - mutum ne "wanda ya ke aiki sakamakon imaninsa ga Allah da ba ya raurawa."

A littafin an hada sakonni, ra'ayoyi da wasiku wadanda Janar Soleimani ya yi, wannan kuwa aiki ne da ya samu goyon bayan gabadaya Imam Mahdi Center.

A cikin shekarar 2020, kwanaki 40 bayan aiwatar da kisan Janar Qassem Soleimani, an sanya daruruwan manyan hotunansa a biranen kasar Italiya. An kuma gudanar da tarurruka a Rome da Milan domin nuna girmamawa ga kwamandan sojan na Iran.

Littafin da Imam Mahdi Center suka rubuta ya ma kunshi jawabi na shugaban juyin-juya hali na kasar Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei da na babban malami, Ayatollah Ali Sistani, a kan shahadar Janar Soleimani. Akwai ma hotuna da ke nuna babban kwamandan sojan na kasar Iran a cikin littafin.

Karshen littafin kuma ya kunshi tarihin rayuwar Janar din kashi-kashi har 20, dangantakarsa da iyalansa da kuma kwamandan fada da 'yan ta'adda na kasar Iraki, marigayi Abu Mahdi al-Muhandis.

No comments

Powered by Blogger.