Header Ads

Hameem Nuhu Muhammad Sunusi ya zama sabon Sarkin Dutse

Sabon Sarkin Dutse, Hameem Nuhu

Hameem Nuhu Muhammad Sunusi ya zama sama sabon sarkin Dutse, bayan rasuwar tsohon sarkin na Dutse, Nuhu Muhammad Sunusi, a cikin satin da ya gabata.

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara, ne ya tabbatarwa da BBC nadin sarautar a ranar Lahadi.

Kwamishinan ya bayyana cewa masu zaben sarki ne suka kaiwa gwamna sunayen masu neman sarautar uku, inda shi kuma ya tabbatar da Hameem Nuhu Muhammad Sunusi, wanda da ne ga tsohon sarkin, a matsayin sabon sarki.

Kwamishinan ya cigaba da bayyana cewa mutane uku da aka kaiwa gwamnan sunayensu sun hada da Galadiman Dutse, Wamban Dutse da kuma shi Hameem wanda shi ne Dan Iyan Dutse kafin nadin nasa.

Masarautar dai za ta sanar da ranar da za ta yi bikin nadin sabon sarkin nan gaba kadan.

Sabon sarkin dai shine babban da ga marigayi sarkin Dutse, Nuhu Muhammad Sunusi, kuma kafin nadin nasa a matsayin sarki ya ruke sarautar Sarkin Dawakin Tsakar-Gida da kuma sarautar Dan Iyan Dutse.

No comments

Powered by Blogger.