Header Ads

Hajjin Bana: Hukumar aikin hajji a Abuja ta bukaci maniyyata da su biya naira miliyan biyu da dubu dari biyar kowannensu

Hukumar aikin hajji ta babban birnin tarayya Abuja ta nemi wadanda ba su samu zuwa aikin hajji a shekarar 2022 ba da su cika kudinsu sukai miliyan biyu da dubu dari biyar (2,500,000). 

Mai kula da bangaren hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Aliyu, ne ya fitar da sanarwar a ranar Laraba a Abuja.

Daraktan hukumar, Nasiru Danmalam ne ya yi kiran a lokacin da yake jawabi ga ma'aikatansu da ke shirin yin ziyara Saudi Arabiya kafin fara gudanar da aikin hajjin.

Ya bayyana cewa sanarwar ta zama wajibi domin a samu sunayen maniyyatan dukkan su, inda ya ce wadanda ba su samu zuwa aikin hajji ba a shekarar 2022 saboda wani dalili, su zo da shaidar biya da suka yi, su bayyana niyyarsu ta zuwa aikin hajjin ko kuma a mayar masu da kudadensu.

Ya bayyana cewa, akwai maniyyata har 185 da suka biya kudin aikin hajji a shekarar 2022, amma ba su samu zuwa ba domin kayyade yawan maniyyata da Saudi Arabiya ta yi.

Maniyyata sama da 1000 ne dai ya bayyana sun yi rijista domin gudanar da aikin na hajji, kuma suna tattaunawa da masu aikin kulawa da maniyyatan domin samar masu da abinci da wurin zama mai kyau a yayin gudanar da aikin hajjin na wannan shekarar.

Ya bayyana cewa a shirye suke su yi duk abinda ya dace domin taimakon maniyyatan kamar yadda hukumar babban birnin tarayya ke bukata.

No comments

Powered by Blogger.