Header Ads

Gwamnonin APC sun yi watsi da wa'adin babban bankin Nijeriya na 10 ga watan Fabrairu

Gwamnonin APC da Buhari a Villa

Gwamnonin da aka zaba a Nijeriya karkashin jam'iyyar APC sun yi watsi da wa'adin 10 ga watan Fabrairu wanda babban bankin Nijeriya ya bayar domin canza kudaden 1000, 500 da kuma naira 200 da sabbin kudaden da ya fitar.

Gwamnonin, wadanda a cikin jihohin Nijeriya 36 su ke mulki a jihohi 21, sun yanke shawarar ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a safiyar ranar Juma'a 10 ga watan Fabrairun 2023 tare da bayyana cewa bayanan da suke samu ya nuna al'ummunsu na shan wahala a cikin kwanakin nan wajen kokarin canza kudaden saboda wa'adin da bankin ya bayar bai zo kan lokaci ba da kuma irin illar da matakin ke yiwa tattalin arzukin kasa.

Kafin su yanke hukuncin ganawar, gwamnonin na APC sun zabi gwamnoni hudu domin ganawa da shugaban babban bankin na Nijeriya, Godwin Emifiele, gwamnonin kuwa sune gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

A yayin ganawar ta su dai sun sanar da shugaban bankin cewa ya gaza wajen aikin da aka ba shi wajen sauya takardun kudin saboda yadda 'yan Nijeriya ke fafutuka wajen cire takardun kudinsu da suka ajiye da kansu a bankunan da ke kasar.

No comments

Powered by Blogger.