Gobarar Monday Market: Gwamna Zulum ya ba da taimakon gaggawa na naira biliyan 1
Bayan faruwar ibtila'in gobara a kasuwar Maiduguri Monday Market a ranar Lahadi da misalin karfe 2 na dare, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a cikin wani jawabi da ya yi a jihar ya bayyana cewa za a bayar da kudi naira biliyan 1 domin taimakon gaggawa ga wadanda ibtila'in ya shafa a yayin da ake cigaba da bincike cikin al'amarin.
Kakakin gwamnan jihar Borno, Malam Isa Gusau, a cikin wata hira da ya yi ya bayyana cewa gwamnan ya gabatar da jawabi lokaci kadan bayan ya ziyarci wurin da al'amarin ya afku, kuma ya umarci sojoji su zo wajen tare da killace shi domin gujewa saba doka da oda.
A cikin jawabin da gwamnan ya gabatar, ya jajantawa mutanen da ibtila'in ya shafa tare da nuna tausayawa a garesu sakamakon dukiyarsu da suka sha wahala a tsawon shekaru masu yawa a kan ta ta salwanta.
A cikin matakan da ya dauka ya tabbatar da cewa za a bada taimakon gaggawa na naira biliyan 1 ga wadanda gobarar ta shafa, kafa kwamiti wanda zai hada da mutane masu kima da kuma wakilan 'yan kasuwar domin sanin abubuwan da aka yi asara da kuma mutanen da suka yi asarar kayan nasu a gobarar, ganawa da shugaban kasa domin neman taimakon gwamnatin tarayya, neman taimakon wasu kungiyoyin agaji da kuma daukar matakai domin magance afkuwar hakan a nan gaba.
Gwamnan ya nemi mutane su kwantar da hankalinsu kuma kada a sa siyasa a cikin al'amarin domin ya faru a lokacin siyasa, inda ya bayyana cewa kasuwar ta taba fuskantar ibtila'in gobara a shekarun baya kuma al'amari ne na bakin ciki.
"Dole za mu yi aiki mu tabbatar da cewa wannan mummunan al'amari bai sake faruwa ba, kuma za mu yi aiki tare ne domin tabbatar da hakan." Gwamnan ya bayyana.
Post a Comment