Header Ads

Gobara a babbar kasuwar Maiduguri ta yi sanadiyyar kona dukiyoyu na miliyoyin naira



Gobara ta tashi a babbar kasuwar da ke garin Maiduguri wadda aka fi sani da Maiduguri Monday Market.

Gobarar, wadda ta tashi da sanyin safiyar ranar Lahadi, ta kona kayayyaki masu yawa wadanda kudin su ya kai miliyoyin naira.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne wajen karfe 2 zuwa 3 na dare, kuma ba a iya gano dalilin ta ba.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels Television ya ruwaito, ba a samu rasa rai ba a yayin gobarar.

Tuni dai gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ziyarci wurin da al'amarin ya afku.

Daraktan kashe gobara na jihar, Umaru Kirawa, wanda ya tabbatar da afkuwar wannan ibtila'i na gobara ga kungiyar dillancin labaru ta Nijeriya (NAN), ya bayyana cewa hukumomin kashe gobara na jihar, kasa da wasu yankunan duk sun hadu domin kawo karshen gobarar.

"Mun baza isassun jami'ai domin kawo karshen al'amarin." Umaru Kirawa ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.