Header Ads

Fiye da mahaddata 50,000 Saudiyya ta yi wa rijista domin gasar karatun Alkur'ani da kiran sallah

Hukumar kula da nishadi ta Saudiyya wato General Entertainment Authority (GEA) ta shirya wata gasa ta karatun Alkur'ani da kiran sallah a kasar, inda aka yiwa sama da mahadda 50,000 daga kasashe 165 rijista.

Gasar, wadda aka bude a ranar 4 ga watan Janairu, ta kasance ta biyu da aka taba gudanarwa kuma itace gasa irinta mafi girma a duniya.

Wadanda suka yi nasara dai a wannan gasa za su samu kyaututtuka da suka kai riyal miliyan 12 jimilla, kuma tuni jami'ai suka fara da tantance mahaddatan da sauran wadanda suka shiga gasar domin zabo wadanda suka cancanci zuwa mataki na gaba.

Akwai dai matakai har guda hudu wadanda mutanen da suka shiga gasar za su fuskanta, inda uku daga cikin wadannan matakai za a yi amfani da wani shafin intanet ne domin masu bibiyar gasar su zabi wadanda suka fi nuna hazaka. 

Mataki na hudu kuwa za a gabatar da su ne a gaban wasu alkalai da kuma 'yan kallo yayin wani shiri na talabijin mai suna Otr Elkalam Show, za kuma a runka haske bangarorin shirin yayin watan Ramadan a tashar MBC.

Wannan gasa dai ta Otr Kalam ta kasance irinta ta farko a duniya wadda ta hada kwarrarun masu kira'ar Alkur'ani da kuma masu kiran sallah a lokaci daya.

No comments

Powered by Blogger.