Header Ads

Dan takarar shugaban kasa a PDP ya yi kira da a saki sakamakon zabe cikin gaggawa


Alhaji Atiku Abubakar na PDP

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi kira da a gaggauta sakin sakamakon zabe a shafin hukumar zabe ta INEC.

Dan takarar shugban kasar ya yi kiran ne ta bakin mai taimaka masa a fannin yada labaru, Paul Ibe, a ranar Lahadi a Abuja.

Dan takarar ya shawarci shugaban hukumar zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, da ya bayar da umarni ga jami'an tattara zabe da su gaggauta sa sakamakon zaben a shafin hukumar.

Ya dai bayyana cewa wannan kira ya zama wajibi domin kaucewa wasu gwamnoni da ke kokarin yin abinda bai kamata ba ga sakamakon a matakin tattara sakamakon na karamar hukuma.

"Ba abu ne mai kyau ga 'yan Nijeriya ba da makomar damakaradiyya a ce an murguda abin da mutane suka nuna sun zaba kamar yadda ya ke a fili a cikin kuru'unsu a jiya." Dan takarar ya bayyana.

Ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu kuma su sa ido sosai ka da su bari makiyan damakaradiyya su hana su abinda suke so, sai kuma ya yi godiya garesu saboda goyon bayan su da yin alkawarin tabbatar da cewa zai cigaba da aiki sosai domin tabbatar da sun cimma bukatunsu.

No comments

Powered by Blogger.