Header Ads

Da gaske ne an kai wa gwamna Mai Mala Buni hari?

Gwamnan jihar Yobe

Gwamnatin jihar Yobe ta musanta kaiwa gwamna Mai Mala Buni hari, inda ta ce sai da gwamnan ya bar wajen taron hayaniya ta barke.

Mamman Mohammed, wanda shine daraktan kafafen watsa labaru ya ce babu wani abu mai kama da haka da ya faru. 

"Mambarin da ake gudanar da taron ne ya cika, lokacin da sanata Ahmed Lawan ke bayani, sai aka ce kowa ya sauka kada ya karye har gwamna da shi sanata.

"Dalilin barin wurin taron da wuri kenan. Muna zuwa wurin wani gidan mai sai muka ji rikici ya barke tsakanin mabiya jam'iyyar tamu." Kamar yadda daraktan ya bayyana.

Mamman ya kara da cewa, "Ba mu ji dadin yadda ake ta yadawa cewa an jefi wasu 'yan jam'iyyarmu a Gashu ba. Sai muka ga ya kamata mu yi magana a kan lamarin domin gudun haifar da abinda ya ke rudani ga jama'a kasar.

"Wannan yakin neman zabe ya gamu da yawan jama'a da ba a taba gani ba a tarihin siyasar garin Gashua. Wannan jama'ar kuwa ta yi maraba da shugaban majalisar dattawa, sanata Ahmed Lawan, gwamna Buni da sauran 'yan kwamitin kamfe.

Daraktan ya bayyana cewa gwamna Buni ya yi tafiya cikin kwanciyar hankali cikin magoya baya, kuma rashin jituwa ce ta faru a tsakanin wasu magoya baya kuma ba ta kai ga hare-hare ga juna ba, wannan kuwa bayan gwamnan da kwamitin kamfe din sun bar wajen ne tuni.

"Masu yada labaran da ba shi kenan ba suna so su nuna cewa ba fahimta mai kyau ne a tsakanin mutanen Gashua da gwamnatin APC a jihar Yobe."

"An cigaba da yakin neman zabe hade da raye-raye, har manyan baki suka bar wajen ba a samu rashin tsaro ba kuma ba wanda aka kaiwa hari." Kamar yadda ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.