Header Ads

Canjin kudi: Kotun kolin Nijeriya ta dakatar da babban bankin Nijeriya aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu

Mai sharia John Okoro na Kotun koli

Kotun kolin Nijeriya da ke Abuja ta dakatar da gwamnatin Nijeriya aiwatar da wa'adin da ta yi wa tsofaffin takardun kudi na 200, 500 da kuma 1000.

Babban bankin dai ya sa wa'adin 10 ga watan Fabrairu ne a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin takardun kudaden.

Gwamnatocin Kaduna, Kogi da Zamfara duka daga arewacin Nijeriya ne dai suka shigar da kara a kotun kolin, suna nema da a hana babban bankin aiwatar da wa'adin na 10 ga watan Fabrairu.

Alkalan kotun bakwai a karkashin jagorancin mai shari'a John Okoro, sun dakatar da gwamnatin Nijeriya, babban bankin Nijeriya da sauran bankunan kasuwanci a Nijeriya aiwatar da wa'adin a cikin hukuncin wucin-gadi da suka yanke, tare da bayyana cewa dole gwamnatin Nijeriya, babban bankin da sauran bankunan kasuwanci a Nijeriya su dakatar da wa'adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin a ranar 15 ga watan Fabrairun shekarar 2023.

Wannan hukuncin dai yana nufin 'yan Nijeriya za su cigaba da amfani da tsofaffin takardun nairar har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukuncin karshe.

No comments

Powered by Blogger.